Kuskuren Cikin Takardun Hukuncin Kano Ba Tuntuben Alkalami ba ne Inji Farfesa Odinkalu

Kuskuren Cikin Takardun Hukuncin Kano Ba Tuntuben Alkalami ba ne Inji Farfesa Odinkalu

  • Farfesa Chidi Odinkalu ya na daga cikin masu ganin ba kuskure kotu ta yi a shari’ar zaben gwamnan jihar Kano ba
  • Masanin shari’ar ya ce abin da ya faru ya fi karfin a kira shi da tuntuben alkalami daga alkalai ko akawun kotu
  • Chidi Odinkalu ya fadawa duniya cewa kotun daukaka kara ba za ta iya yin tafka da warwara kuma ta gyara yanzu ba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada.

Kano - Chidi Odinkalu ya yi karin haske game da bayanai masu cin karo da juna da aka samu a takardun hukuncin shari’ar gwamnan Kano.

Farfesa Chidi Odinkalu ya zanta da tashar Channels TV a ranar Laraba, ya nuna sam bai yarda a ce tuntuben alkalami aka samu daga kotu ba.

Kara karanta wannan

Mataimakin Sanusi a bankin CBN ya fito ya soki hukuncin zaben gwamnan jihar Kano

A wasu wuraren, bayanan da aka fitar a takardun CTC da farko sun nuna NNPP ce ta samu nasara a kotu, masanin shari’ar ya ce da walakin.

Gwamnan Kano
Kotu ta tsige Gwamnan Kano Hoto: @KYusufAbba
Asali: Facebook

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

CTC: Ana gyara kuskure a kotu?

Farfesa Odinkalu ya ce akwai dokar tuntube a kotu wanda ake amfani da ita wajen gyara kananan kura-kurai da aka yi wajen rubuta hukunci.

Amma ganin yadda aka rika samun tafka da warwara a takardun CTC na shari’ar Kano, tsohon shugaban na NRHC ya ce abin ya wuce kuskure.

Shari'ar zaben Kano ba kuskure ba ne

"Sam ba tuntuben alkalami ba ne, akwai doka a aikin shari’a da ake amfani da ita wajen kuskuren alkalami.
Ana kiran ta dokar tuntube, misali idan za a rubuta Wi-Fi sai aka rubuta Wi-Fe, za a iya gyara wannan kuskure.
Kotu za ta sanar da wadanda ake shari’a da su, sai a gyara.

Kara karanta wannan

APC ta yi watsi da takardar CTC da ke tabbatar da Abba a matsayin gwamnan Kano: "Kuskure ne"

Amma ba za ta yiwu ka ce a biya ni wasu kudi kuma sai ka dawo ka ce za a gyara, dayan bangaren ne zai biyya.
Ko kuwa a ruguza hukuncin karamar kotu a rubuce sai kuma daga baya a ce kuskure ne, ba zan yarda ba.
Wadannan ikirari ne, hukuncin kotu aka zartar, yadda za a warware matsalar ita ce sake duba shari’ar idan da lokaci.
Ko kuwa ayi nazarin shari’ar kafin a tafi kotun koli. Wannan ba kuskuren alkalami ba ne, abin da aka koya mani kenan.

- Chidi Odinkalu

Bulama Bukarti wanda lauya ne da yake kasar waje, ya ce tun da yake karatun ilmin shari’a bai taba cin karo da irin wannan katabora ba.

A wani bidiyo da ya wallafa a shafinsa, lauyan ya soki yadda aka yi wannan kuskure da ya ce ba zai gyaru ba duk da yarda APC ta yi nasara.

Kara karanta wannan

Labari Mai Zafi: Lauyoyin NNPP Sun Daukaka Kara a Kotun Koli Kan Tsige Abba

Lauya ya ce an tsige Gwamnan Kano

An ji labari cewa wani lauya mai kare hakkin jama’a ya yi bayanin abin da ya jawo sabani a takardun hukuncin zaben Gwamnan na Kano.

Abba Hikima ya ce gaskiyar magana ita ce Gwamna bai iya samun nasara a kotun daukaka kara ba duk da kuskuren da yake cikin CTC.

Asali: Legit.ng

Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng

Online view pixel